Brazil: Thiago Alcantara ba zai buga gasa ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a yiwa Thiago Alcantara tiyata a gwiwa

Dan wasan tsakiyar Bayern Munich Thiago Alcantara ba zai kasance cikin tawagar 'yan wasan Spain da zasu buga gasar cin kofin duniya ba, saboda raunin da ya samu a gwiwar sa.

An sanya suna dan wasan mai shekaru 23 a cikin tawagar Spain a ranar Litinin, amma yana bukatar ayi masa tiyata a gwiwa, bayan raunin da ya samu a wannan mako.

An ambato babban jam'in kulab din Bayern Karl-Heinz Rummenigge ya na cewa 'babu dadi kuma na tausaya masa'.

Spain na cikin rukunin B tare da kasashen Netherlands da Chile da kuma Australia.