Tyson na shirin kyautar da kambunsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Furry ya riki kambun nahiyar Turai

Shaharren da wasan damben Boxing din nan Tyson Fury ya sha alwashin mika wa Dereck Chisora kambunansa da yaci a gasar Ingila da kasashen turai matukar dan wasan ya sami nasara a kansa, a fafatawar da za su yi ranar 26 ga watan Julin wannan shekara.

Fury mai shekaru 25, za su hadu da Briton a Manchester, wanda kuma ya yi nasara daga cikin su, ana sa ran za su kara da Wladimir Klitschko a gasar IBF, WBA da kuma WBO

Tyson ya fadawa BBC cewa "da zarar na lakada masa na jaki, zan ba shi kambun domin ni na wucce wannan matsayin."

Chisora mai shekaru 30 wanda ya riki kambun nahiyar turai ya yi rashin nasara a hannun Fury da yawan maki a bugawar da suka yi a shekarar 2011.

Sai dai har yanzu a iya cewa kambun na mai rabo ne.