Messi ya sabunta kwangilarsa a Barca

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan Barcelona

Lionel Messi daya daga cikin zaratan 'yan kwallo a duniya ya amince da kulla sabuwar yarjejeniya da Barcelona.

Dan kasar Argentina din a watan Fabarairun da ya wuce ne, ya amince da sabuwar yajejeniyar har zuwa shekara ta 2018.

Kawo yanzu dai ba a san tsawon yarjejeniyar da aka kulla da Messi ba, mai shekaru 26 wanda ya zura kwallaye 41 cikin wasanni 43.

Sanarwa daga Barcelona ta ce "Nan da kwanaki masu zuwa za a sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar".

Rahotanni daga kafafen yada labarai a kasar Spain sun ce Messi wanda ya samu kyautar gwarzon dan kwallon duniya har sau hudu, zai dunga karbar kusan Euro miliyan 20 a kowacce kakar wasa har zuwa watan Yunin 2019.

Karin bayani