'Yan wasa 8 za su bar Middlesbrough

Frazer Richardson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Middlesborough ta bayar da aron Richardson ga kulob din Ipswich

Kungiyar kwallon kafa ta Middlesborough, ta fitar da sunayen 'yan wasa takwas da ba za a sabunta kwantiraginsu ba a lokacin bazara.

'Yan wasan sun hada da Frazer Richardson mai shekaru 31, wanda ya shiga kulob din a watan Augusta, kuma ya buga wa kulob din wasanni 11.

Stuart Parnaby mai shekaru 31, ya sake koma wa kulob din a karo na biyu a watan Augustan shekarar 2012, inda ya yi wasanni 21, uku daga cikinsu a shekarar 2013 zuwa 2014.

Sauran 'yan wasan sun hada da Jayson Leutwiler da Lewis Sirrell da Birger Meling da Jake Fowler da Cameron Park da kuma Matthew Waters.