Manyan kulob-kulob na harin Ramsey

Aaron Ramsey Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aaron ya taba karyewa a kafa a shekarar 2010 kuma sai da ya yi shekara guda kafin ya warke

Tsohon dan wasan kungiyar Arsenal, John Hartson ya ce Aaron Ramsey na cikin 'yan wasan da ake sa ran manyan kugiyoyin kwallon kafa za su yi rububin sayansu.

Ramsey mai shekaru 23 yana fatan samun damar kulla wata alaka da Arsenal, a lokacin haduwarsu da Hull ranar asabar a wasan karshe na FA.

Hartson ya ce "Tabbas Aaron zai yi alaka da wasu shahararrun kungiyoyin kwallon kafa 10 a wannan bazara, sai dai bana jin zai bar Arsenal nan kusa."

Hartson ya kwashe shekaru biyu a Arsenal, inda ya samu nasarar zura mata kwallaye 51 ya kuma kara da cewa, "Aaron babban dan wasa ne, saboda haka Arsenal ba za ta yarda ta yi asararsa ba."