Arsenal ta lashe kofin FA

Image caption Saura kadan wankin hulla ya kai Arsenal dare a yayi wasan karshen

Kungiyar Kwallon kafa Arsenal ta lashe gasar kofin kalubale ta kasar Ingila wato FA Cup a karon farko cikin shekaru 9.

Arsenal ta doke Hull City ne da ci 3-2 a wasan karshen na gasar da aka buga a filin wasa na Wembley da yammacin ranar Assabar.

Sakamakon wasan karshen dai ya zo da mamaki ganin yadda Hull City ta jefa wa Arsenal kwallaye 2 a raga cikin mintuna 10 na farkon wasan; amma sai Arsenal ta farfado bayan da Santi Carzola ya ci mata kwallo ta farko kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Laurent Koscielny ya kara ci mata ta 2 a minti na 71 kafin Aaron Ramsey ya jefa kwallo ta 3 ana gab da tashi.

Arsenal ta dauki kofin har sau 5 a baya a karkashin Aresne Wenger, amma wannan ne karon farko da Hull ta buga final na FA din.

Karin bayani