Atletico Madrid ta dauki La Liga

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nasarar ta kawo karshen kaka-gidan da Barcelona da Real Madrid ke yi a gasar La Liga

Kungiyar Atletico Madrid ta dauki kofin gasar La Liga a karon farko tun 1996 bayan ta yi kunnen doki 1-1 da Barcelona.

Alexis Sanchez ne ya fara jefa kwallo ragar bakin minti 33 da fara wasa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 49 Godin ya rama wa Atletico Madrid.

Zakarun sun kammala gasar mai wasanni 38 da maki 90, wato bambamcin maki uku tsakaninta da Barcelona ta biyu da Real Madrid ita ma ta uku.

Kofin Kalubale na Jamus

A Jamus kuwa Bayern Munich ta dauki Kofin Kalubale na kasar da ta hada da na Bundesliga bayan da ta buge Borussia Dortmund 2-0,

a wasan da aka shiga karin lokacin fitar da gwani.