Gerardo Martino zai bar Barcelona

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A wasanninsa 59 ya yi nasara a 40, amma ya kasa daukar kofin cikin gida ko na Turai.

Kocin Barcelona Gerardo Martino zai ajiye aiki bayan ya kasa daukar Kofin La Liga ko wani kofi tun da ya maye gurbin marigayi Tito Vilanova a watan Yuli .

Kocin da kungiyar sun amince da matakin da ya dauka bayan a karon farko tun 2007-08 kungiyar ta kammala kaka ba tare da daukar wani babban kofi ba.

Martino dan Argentina mai shekara 51, ya ce,'' ina ba da hakuri saboda kasa cimma burin kungiyar.

Ina godiya ga kungiyar da 'yan wasan kan yadda suka yadda da ni.''

A wasanninsa 59 ya yi nasara a 40, amma ya kasa daukar kofin cikin gida ko na Turai.

Tsohon dan wasan Barcelona Luis Enrique, wanda zai bar aikin kocin Celta Vigo a bana shi ake ganin zai gaji Martino.

Karin bayani