Mai tsaron gidan Faransa ba zai shiga gasa ba

Image caption Akwai yiwuwar Stephane Ruffier na St Etienne ne zai maye gurbin Mandanda

Mai tsaron gidan Faransa Steve Mandanda ba zai buga gasar cin kofin duniya ba saboda raunin wuyansa.

Dan wasan mai shekaru 29 wanda shine na biyu dake bin Kyeptin din Faransan Hugo Lloris, ya samu rauni a wuyansa a lokacin da suke wasa da Marseille a ranar Asabar.

Mandanda ne ya tabbatar da wannan matsayi a shafin sa na Twitter yana mai cewa 'abin bakin ciki ne nake sanar da ku cewa ba zan iya kasancewa cikin wasan kofin duniya ba'

Akwai yiwuwar Stephane Ruffier na St Etienne ne zai maye gurbin sa.