ManU ta dauki Vanja Milinkovic

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Kulab din Man U ya sayi dan wasa na farko tun bayan korar David Moyes

Manchester United ta dauki mai tsaron gidan Serbia Vanja Milinkovic

Wannan shine dan wasan da kulab din ya saya a karon farko tun bayan korar David Moyes a watan da ya gabata.

Sai dai, Milinkovic, dan shekaru 17, zai kasance da FK Vojvodina a kakar wasanni mai zuwa.

Nemanja Vidic da kuma Zoran Tosic sune sauran 'yan wasan Serbia da suka yiwa ManU wasa.