Finke zai karawa 'yan wasan Kamaru azama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Volker ya sha alwashin ganin an samu fahimtar juna a tsakanin 'yan wasan

Kocin kungiyar wasan kwallon kafa ta Kamaru Volker Finke, ya ce zai karawa 'yan wasan sa azama a mako mai zuwa a filin wasa dake Kasar Autralia, inda suke karbar horo a shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin duniya.

Gwiwar Kulob din na Indomitable Lion ta yi laushi ne, bayan da kasar Portugal ta casa ta da ci 5-1 a watan Maris da ya gabata.

Volker ya kuma sha alwashin ganin an samu fahimtar juna a tsakanin 'yan wasan.

Kulab din Indomitable Lions zai yi wasa tare da Macedonia da Paraguay a wasan sada zumunta a Kufstein ranar 26 ga watan Mayu da kuma 29 ga watan na Mayu.

Sai kuma su tunkari Jamus ranar 1 ga watan Yuni.