Giggs ya yi ritaya daga Man U

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Giggs ne dan wasan da ya fi kowanne karbar kyaututtuka a Ingila.

Dan wasan Manchester United Ryan Giggs ya bayyana ritayar sa ne bayan da aka bashi mukamin mataimakin sabon mai horas da 'yan wasa Louis Vaan Gaal.

Dan wasan mai shekaru 40 ya buga wasanni 963 a zaman sa a United, yayin da ya yiwa Wales wasanni 64.

Giggs shi ne dan wasan da ya fi kowanne karbar kyaututtuka a Ingila, sakamakon nasarorin da ya yi na cin gasar wasanni 13 da kofin FA 4 da kofin gasar zakarun turai 2 da sauran lambobin yabo.

Dan wasan ya ce "Yau rana ce mai cike da matukar alfahari da bakin ciki, amma kuma mafi soyuwa a rayuwata ta nan gaba."

Yace koda yaushe mafarki na shine, bugawa Manchester United wasa, amma duk da bakin cikin daina sa rigar United, na yi nasara matuka kasancewar na yi wasa da shaharrarun 'yan wasa na duniya tare da yin aiki da gwarzon koci Sir Alex Fergusan da kuma bugawa kulob din da yafi farin jini a duniyar kwallon kafa.