Roberto Landi zai koma Liberia

Image caption An kori Landi a watan Fabrairun shekarar 2012

Hukumar Kwallon kafa Liberia zata tattauna tare da Kochin Italiya Roberto Landi game da yiwuwar sake komawa domin jan ragamar Lone Star.

An kori Landi a watan Fabrairun shekarar 2012 bayan ya shafe kasa da shekara guda da su.

Ya ci wasanni biyu kachal a wasannin takwas da ya jagoranta.

Ana tsammanin tsohon mai tsaron gidan zai isa Monrovia a ‘yan kwanaki masu zuwa domin tattauna dawowar sa.