'Lashe kofin FA ya bamu kwarin gwiwa'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan Arsenal na murnar wannan nasarar

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce lashe kofin FA ya maidowa kungiyar tagomashinta, tare da fatan samun nasarori a gaba.

Arsenal ta lashe kofin FA bayan ta doke Hull City a wasan karshe wanda shi ne kofi na farko da kungiyar ta samu cikin shekaru tara.

Wenger ya ce "Kofin na da mahimmanci ga tarihin kungiyar".

Arsenal ta sha suka a shekarun baya saboda kasa lashe kowanne kofi a cikin shekaru masu yawa.

Arsene Wenger ya tabbar da cewa zai sabunta kwangilarsa a kungiyar da yake jagoranta tun a shekarar 1996.

Karin bayani