Ashley Cole zai bar Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ashley Cole ba zai je Brazil ba

Ashley Cole ya ce baya tunanin zai ci gaba da kasancewa a Chelsea a kakar wasa mai zuwa bayan shafe shekaru takwas a Stamford Bridge.

Dan kwallon mai shekaru 33, a farkon wannan watan ya sanar da cewar zai daina bugawa Ingila kwallo baya taka leda a wasanni 107.

Cole ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar "Ina duba zabin da nake da shi domin buga kwallo a kakar wasa mai zuwa".

Dan wasan ya taimakawa Chelsea ta lashe gasar Premier a shekara ta 2010 da kuma na Zakarun Turai a 2012.

A shekara ta 2006 ne ya koma Chelsea daga Arsenal.

Karin bayani