Lius Enrique ne sabon kocin Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lius Enrique na da farin jini a Nou Camp

An nada Luis Enrique a matsayin sabon kocin Barcelona a yarjejeniyar shekaru biyu.

Dan shekaru arbai'in da hudu, Enrique ya ja ragamar karamar tawagar Barca daga shekara ta 2008 zuwa 2011 kafin ya koma kungiyar Celta Vigo.

Ya maye gurbin Gerardo Martino wanda ya bar Barcelona bayan kungiyar ta kasance ta biyu a teburin gasar La Liga.

Martino ne ya maye gurbin Tito Vilanova a shekara ta 2013 amma ya kasa taka rawar gani a kungiyar.

Enrique tsohon dan kwallon Barcelona ne wanda ya buga wa kungiyar wasanni 300 daga shekarar 1996 zuwa 2006.

Nada Lius Enrique ya zo rana guda da Barcelona ta sayi golan Borussia Monchengladbach Marc-Andre Ter Stegen sannan kuma Lionel Messi ya sabunta kwangilarsa da kungiyar.

Karin bayani