Claurido Ranieri ya bar Monaco

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mataimakin Shugaban Kulab din ya yabawa Ranieri

Claudio Ranieri ya bar kulab din Monaco na Faransa bayan ya shafe shekaru biyu a matsayin kocin 'yan wasa.

Tsohon Manajan Chelsea din ya jagoranci kulab din zuwa mataki na biyu a kan tebur inda Paris St-Germain ta lashe gasar.

Mataimakin Shugaban Kulab din Vadim Vasilyev ya ce aikin dan kasar Italiyan ya yi kyau sosai.

Attajirin Rasha, Dmitry Rybolovlev shi ne mai mallakar kulab din bayan ya saye shi a watan Disambar shekarar 2011.