Ronaldo da Bale za su yi wasan karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid za ta yi wasa da Atletico Madrid ranar asabar

Cristiano Ronaldo da Gareth Bale na da koshin lafiyar da za su iya yiwa Real Madrid wasan karshe na gasar zakarun Champions League a ranar Asabar da Atletico Madrid.

Ronaldo mai shekaru 29 bai samu damar bugawa Real Madrid wasannin da tayi a baya ba guda biyu, yayinda shima Bale mai shekaru 24 bai kasance a atisayen da suka yi ba a ranar Talata

'Yan wasan biyu zasu taka wasa kuma lashe kofi shine abu mafi mahimmanci a gare mu' in ji Manaja Carlo Ancelotti.

Sai dai babu tabbas ko dan wasan baya Pepe da na gaba Karim Benzema zasu taka wasan karshen.

Real Madrid na neman lashe kofin a karo na 10