Pique zai ci gaba da murza leda a Barca

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pique tare da abokiyar zamansa, shahararriyar mawakiya Shakira

Dan kwallon Barcelona Gerard Pique ya amince ya tsawaita kwangilar karin shekaru hudu don ci gaba da taka leda a Nou Camp.

Nan da 'yan kwanaki dan wasan mai shekaru 27 zai sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar har zuwa shekara ta 2019.

Pique ya buga kwallo a Manchester United daga shekara ta 2004 zuwa 2008.

Dan wasan, ya bugawa Barca wasanni 266, inda ya lashe kofunan gasar La Liga hudu da kuma na Zakarun Turai sau biyu.

Wannan sanarwar kan Pique na zuwa ne kwana daya bayan da Lionel Messi ya sabunta kwangilarsa sannan kuma aka nada Luis Enrique a matsayin sabon koci.

Karin bayani