Van Gaal na hangen nasara a Old Trafford

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Van Gaal ne zai jagoranci Holland a gasar kofin duniya

Sabon kocin Manchester United, Louis van Gaal ya ce yanason ya samu nasara a Old Trafford kamar yadda ya samu a Barcelona da Bayern Munich.

Dan kasar Holland din ya lashe gasar La Liga tare da Barcelona a shekarar 1997-1998 sannan kuma ya lashe gasar Bundesliga tare da Bayern Munich a shekara ta 2009-10.

Manajoji uku da suka lashe gasar Premier a karon farko da zuwarsu, su ne Jose Mourinho da Carlo Ancelotti a Chelsea da kuma Manuel Pellegrini a Manchester City.

Van Gaal ya ce "Zan yi murna idan na lashe gasar Premier a shekarar farko".

Van Gaal ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru uku tare da Manchester United, kuma ya taba lashe gasar kwallo sau bakwai a kungiyoyi hudu watau Ajax da Barcelona da AZ Alkmaar da kuma Bayern Munich.

Karin bayani