Ingila na koyon jure zafin Brazil

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana sa ran yawan zafi a birnin Manus ya kai awo 30 a watan Yuni.

'Yan wasan kasar Ingila da za su je Gasar cin Kofin Duniya a Brazil na atisaye saye da taguna masu yawa domin shiryawa yadda zasu jure yanayin zafin kasar.

Wasu kwararrun daga jami'ar Loughborough ne ke taimakawa wajen lura da karfin juriyar 'yan wasan a sansanin da suke karbar horo a kasar Portugal.

''Mun jarraba yawan zufan da za su fitar, da yadda za su iya farfadowa idan zafi ya galabaitar da su da kuma irin taimakon da za a yi musu.'' inji Kocinsu Roy Hodgson.

Ingila za ta fara karawa ne da Italiya a wasan farko na rukuni D a birnin Manaus ranar 14 ga watan Yuni, kafin karawa Uruguay da Costa Rica.

Karin bayani