Suarez ya ji rauni a gwiwarsa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Gwarzon dan kwallon Premier na bana.

Kafofin yada labarai a Uruguay sun ce Lius Suarez ya ji rauni a lokacin horo kuma watakila ba zai buga gasar cin kofin duniya a Brazil ba.

Rahotannin sun ce dan kwallon Liverpool din mai shekaru 27 za a yi masa tiyata a ranar Alhamis saboda rauni a kafarsa.

An kiyasta cewar zai iya jinyar akalla kwanaki 15 zuwa makonni hudu.

Uruguay za ta fuskanci Ingila a gasar kofin duniya a ranar 19 ga watan Yuni a birnin Sao Paulo.

Karin bayani