Rooney na son ya zama kyaftin

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wayne Rooney da Van Persie

Wayne Rooney ya ce yana saran a nada shi kyaftin din Manchester United, duk da rahotanni na cewar Robin van Persie ne zai zama kyaftin.

A yayinda Nemanja Vidic zai bar kungiyar, sabon kocin tawagar, Louis van Gaal zai nada sabon kyaftin bayan kamalla gasar cin kofin duniya.

A yanzu haka Van Persie ne kyaftin din Netherland da Van Gaal ke jagoranta.

Rooney ya ce "Ina son in zama kyaftin, ina ganin na shirya. Sai dai batun ra'ayin koci ne".

Vidic wanda ya jagoranci United tun daga shekara ta 2010, zai koma Inter Milan, sannan mataimakinsa, Patrice Evra shi ma zai bar kungiyar.

Karin bayani