Yau ne wasan karshe na Champions League

Gasar champions league Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama dai na son ganin wasan na kasrhe, da su ke fatan gwanayensu za su taka muhimmiyar rawa a wasan.

To a yau ne ake buga wasan karshen na gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na Turai wato Champions League.

Za a buga wasan karshen ne a birnin Lisbon na kasar Portugal tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid dukkansu daga kasar Spain.

Tun a jiya Jumu'a ne dubban yan kasar Spain suka kwarara zuwa birnin na Lisbon domin kallon wasan karshen.

A nahiyar Afrika ma inda kungiyoyin biyu ke da dimbin magoya baya, masu sha'awar wasan kwallon kafa sun zaku su kalli wasan karshen.