Bale:har abada ba zan manta da nasarar ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bale ya barar da dama da yawa kafin ya ci wa Real Madrid kwallo ta biyu

Gareth Bale ya ce nasarar daukar kofin Zakarun Turai da suka yi za ta kasance da shi har abada bayan da ya taimaka wa Real Madrid ta doke Atletico Madrid 4-1 wasan karshe.

Ya ce, '' abin da kowana danwasan kwallon kafa ke fata ne amma kuma ba ko da yaushe hakan ke samuwa ba a wasan kungiya.

Bale mai shekara 24 , ya ce, ''murnar magoya bayan abun alfahari ne gare ni amma abu mafi muhimmanci shi ne mun yi aiki tukuru tare kuma muka daukar wa kungiyar kofin na goma.

Dan wasan ya kuma bayyana cewa idan dawowarsa Real Madrid za ta sa su rinka daukar kofuna to da ko a kan kuin da bai taka kara ya karya ba zai dawo.

Karin bayani