Tennis: Federer da Serena sun yi nasara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cikin mintina 84 Federer ya buge Lukas Lacko

Roger Federer ya yi nasara a gasar tennis ta Faransa wato Roland Garros inda ya doke Lukas Lacko.

Dan wasan na hudu a duniya wanda sau 17 yana cin babbar gasar tennis ya yi galaba a kan Lacko dan Slovakia da ci 6-2 6-4 6-2.

Federer zai kara a gaba da Diego Sebastian Schwartzman na Argentina wanda ya yi nasara a kan Gastao Elias na Portugal da ci6-4 6-2 75.

Ita kuwa Serena Williams ta fara kare kambin ne na gasar ta Faransa da take rike da shi da nasara a kan Alize Lim 'yar Faransa da ci 6-2 6-1.

'yar wasan ta daya a duniya a bangaren mata ta na neman daukar kofin ne a karo na uku.