Cardiff za ta dauki Macheda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Macheda ya yi zaman aro a Stuttgart ta Jamus da Sampdoria ta Italia da QPR da kuma Doncaster Rovers.

Ana saran Cardiff City za ta dauki tsohon dan wasan Manchester City na gaba Federico Macheda.

Dan wasan mai shekaru 22 dan kasar Italiya zai koma kungiyar ne bayan Man United ta sake shi.

Kocin Cardiff Ole Gunnar Solskjaer ya koyar da Macheda a tawagar 'yan wasan ko-ta-kwana na Man United kafin ya samu shiga cikin babbar tawagar yana dan shekara 17.

Macheda ya yi kakar wasannin da ta wuce a zaman aro a kungiyar Bermingham ta kasa da Premier inda ya ci kwallaye 10 a wasanni 18.

Tsohon matashin dan wasan na Lazio ya yi fice ne a Old Trafford tun lokacin da ya ci Aston Villa a watan Afrilu na 2009 ana dab da tashi daga wasan.

Duk da wannan fice yana matashi, Macheda ya yi fafutukar samun shiga jerin fitattun 'yan wasan Man United da ke wasa akai-akai a shekarun nan.

Kuma ya yi zaman aro a Stuttgart ta Jamus da Sampdoria ta kasarsa Italia da kungiyar QPR da kuma Doncaster Rovers.