Gareth zai kara kaimi - Ancelotti

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ancelotti ya ce Gareth Bale ya yi rawar gani

Manajan Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya ce dan wasan kungiyar Gareth Bale zai kara kaimi a taka leda a kakar wasa ta badi bayan namijin kokarin da ya yi a bana.

Bale, mai shekaru 24, ya zura kwallo a wasan karshe na Gasar zakarun Turai da kungiyar ta doke Atletico Madrid da ci 4-1, sannan ya ci kwallon da ta ba su nasara kan Barcelona a gasar Copa del Rey.

Ya bayyana haka ne a gaban dubban magoya bayan kungiyar lokacin da yake nuna musu irin nasarorin da suka samu a bana.

Bale ya koma Real daga Tottenham a kakar wasa ta bara kan kudi £85.3m.

Ancelotti ya ce, "Gareth ya kwashe kakar wasa ta bana yana taka leda mai kyau, kuma zai kara kaimi a kakar wasa ta badi''.