Rodgers ya sabunta kwantiragi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rodgers, ya ce, ''Ina farin cikin dorawa a kan ginshikin da muka fara ginawa shekaru biyu da suka gabata''

Kociyan Liverpool Brendan Rodgers ya sabunta kwantiraginsa da kungiyar da ta zo ta biyu a gasar Premier da ta kare na wani tsawon lokaci.

Rodgers wanda ya gaji Kenny Dalglish a 2012, ya jagoranci kungiyar ta sake samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai bayan shekaru hudu da ta rasa hakan.

Kociyan dan Arewacin Ireland mai shekara 41 ya ce, '' na yi matukar farin ciki da wannan giramamawa da aka yi min ta kara min wa'adin cigaba da zama a wannan shahararriyar kungiya.''

Zakarun na Ingila sau 18 na gaba-gaba wajen damar daukar kofin Premier na bana kafin Chelsea ta bisu har gida ta casa su 2-0.

Duk da rashin daukar kofin na Premier tsohon kocin na Swansea, Brendan Rodgers ya zama zakaran kociyoyi na gasar ta Premier na bana.