Tottenham na tattaunawa da Pochettino

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yanzu dai bai fi shekara daya ya rage masa kwantaraginsa ta kare ba da Southampton.

Kocin kungiyar Southampton , Mauricio Pochettino na kan tattaunawa da kulob din Tottenham don zama sabon kocin kungiyar.

Spurs dai ta sha kokarin samun sabon kocin da zai jagoranci kungiyar tun bayan da ta kori kocinta Tim Sherwood a farkon wannan watan.

Pochettino mai shekaru 42, ya karbi jagorancin kungiyar Southampton a watan Janairun 2013, inda ya maye gurbin Nigel Adkins ya kuma kai kungiyar ga mataki na 8 a gasar premier.

Kocin dan kasar Argentina, a farkon watannan ne ya bayyana cewa ya shirya don tattaunawa kan makomarsa a karshen kakar bana, Inda aka fara rade-radin cewa zai bar kungiyar Southampton.

Kocin ya ce yanzu yana jiran ji daga bakin sababbin shugabannin kungiyar kafin ya yanke hukunci kan makomarsa.