Djokovic da Saharapova sun yi nasara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Idan Djokovic ya dauki kofin gasar zai iya kafa tarihin buga babbar gasa ta duniya

Maria Sharapova ta doke Ksenia Pervak ta kai zagaye na biyu na gasar Tennis ta Faransa, Roland Garros da ci 6-1 6-2.

Sharapova 'yar Rasha ita ce ta bakwai a jeren gwanayen tennis mata a duniya.

'yar wasan wadda ta dauki kofin gasar a 2012 ta buge Ksenia Pervak wadda ita ma 'yar Rasha ce a rana ta biyu ta gasar, cikin sauki.

Yanzu Sharapova za ta kara da Tsvetana Pironkova ta Bulgaria amma kuma da alamu za ta hadu da Serena Williams a wasan dab da na kusa da karshe.

Shekaru biyu da suka wuce Serena ta doke ta a wasan karshe na gasar ta 2013.

Novak Djokovic

Shi ma Novak Djokovic dan Serbia tsohon na daya a duniya ya samu nasarar shiga zagaye na biyu na gasar ta Faransa bayan ya doke Joao Sousa na Portugal da ci 6-1 6-2 6-4.