Tom Ince na san bin sahun Mahaifinsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption dan wasn da ke kokarin taka sawun mahaifinsa a sha'anin kwallon kafa.

Alamu na nuni da cewa Tom Ince, wanda kwantaraginsa ta kare a kulob din Blackpool na kara himma wajen bin sawun mahifinsa a kokarin da yake na buga wa Inter Milan wasa a gasar badi.

Tom, dan wasan gefe mai shekaru 22 da mahaifinsa ,paul, sun isa Milan ranar Lahadi don tattauna batun komawarsa kulob din.

Mahaifin dan wasan na gefe, wato Paul, ya shiga kulob din Inter Milan a shekarar 1995 bayan da ya baro kulob din Man United.

Dan wasan ya ce, "Inter Milan na da karfi kuma Italiya babbar kasa ce, ina kuma da abubuwan kauna masu yawa da nake tunawa."