Wales za ta yi wasa ba Bale

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wales din ta samu karin karfi a farkon makon nan da dan wasan baya Chris Gunter

Kungiyar kwallon kafa ta Wales za ta yi wasan sada zumunci da Netherlands ba tare da shaharraren dan wasanta ba Gareth Bale a ranar 4 ga watan Yuni a birnin Amsterdam.

Wales ta tabbatar da cewa dan wasan gaban Real Madrid mai shekaru 24 na fama ne da ciwon kafa makonnin da suka gabata.

Bales maciyin kwallo ne, ya kuma taimaka wa Real Madrid a nasarar da ta samu kan Atletico Madrid a gasar Zakarun Turai da aka kammala makon da ya gabata.

Haka kuma Wales din za ta yi wasan ba tare da Aaron Ramsey ba saboda yana hutu.