Kofin Duniya: Brazil ta fara atisaye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Brazil na adawa da yawan kudin da ake kashe wa gasar ta kofin duniya

Kungiyar kwallon kafa ta Brazil ta fara motsa jiki a shirye-shiryenta na tunkarar gasar cin kofin duniya duk kuwa da zanga-zangar da ke gudana a Rio de Janeiro.

Wasu malaman makaranta da ke yajin aiki sun tare wata motar bus mai dauke da 'yan wasan na Brazil inda suka rinka fadin kalamai marassa dadi dangane da gasar.

Amma daga baya, 'yan wasan sun samu tarba daga magoya baya da ma wasu ma su zanga-zangar lokacin da suka isa filin wasa na Granja.

Dubban masu zanga-zanga ne dai suka fito don nuna kin jinin gasar da za a fara a wata mai zuwa.