Zuciyata na tare da Ingila- Lallana

Image caption ''Shekaru hudu da suka wuce ni da abokanaina mun kasance 'yan kallon gasar ta kofin duniya''

Dan kwallon Southampton Adam Lallana ya ce cece-kuce game da makomarsa ba zai shafi wasansa tare da Ingila ba.

Dan shekaru 26, wanda Liverpool ke zawarcinsa, ya ce a yanzu ya mai da hankali ne a kan gasar cin kofin duniya da za a soma a ranar 12 ga watan Yuni.

Lallana ya ce "Ko an fayyace inda zan koma ko ba a fayyace ba, hankalina na tawagar Ingila.''

Lallana ya koma Southampton ne a shekara ta 2000 kuma ya zura kwallaye 10 a wasanni 42 a kakar wasa ta bana inda kungiyar ta karke a matsayin ta takwas a kan tebur.

Karin bayani