Tottenham ta dauki Pochettino koci

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kociyan ya zama na goma ke nan da kungiyar ta Tottenham ta dauka tun 2001.

Tottenham ta dauki kocin Southampton a matsayin sabon kociyanta na tsawon shekaru biyar.

Pochettino mai shekara 42 ya maye gurbin Tim Sherwood wanda ya rike kungiyar tun watan Janairu kuma aka sallame shi a karshen kakar bana, bayan ya maye gurbin Andre Villas-Boas.

Tottenham ta kammala gasar Premier da ta kare a matsayi na takwas da hakan ya sa ta samu gurbin gasar Europa.

Ita kuwa Southampton ta kammala gasar ne a matsayin ta takwas bayan da Pochettinon ya kai ta matsayi na 14 a 2013.