Tennis: Watson ta kai zagaye na biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana ganin Watson za ta iya sake kwato matsayi na daya a Birtaniya daga Laura Robson wadda ta ji rauni.

'Yar wasan tennis ta Ingila Heather Watson, ta doke Barbora Zahlavova Strycova a gasar Roland Garros ta samu nasarar kaiwa zagaye na biyu da ci 6-3 da 6-4.

Watson ta biyu a jerin gwanayen wasan mata a Ingila, ta ci wasanni 11 a watan Mayu kadai, bayan nasarar da ta samu a gasar Prague.

Kafin karawar tasu ana ganin Watson ta 92 a duniya da wuya ta iya galaba a kan Zahlavova Strycova wadda ke matsayi na 63.

Heather mai shekaru 22, 'yar Guensey, za ta hadu nan gaba da Simona Halep 'yar kasar Romania a gasar ta Farsansa