Mai kungiyar Man United ya mutu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutuwar attajirin ba za ta yi tasiri sosai a kan mallakar kungiyar ba saboda iyalansa ne ke da kashi 90 cikin dari na hannun jarinta

Mutumin da ya mallaki kungiyar Manchester United attajiri Malcolm Glazer dan kasar Amurka ya mutu yana da shekara 85.

Iyalan Glazer sun sayi kungiyar ta Manchester United a kan fam miliyan 790 a watan mayu na 2005.

Duk da adawar da magoya bayan kungiyar ta Premier su ka nuna kan cinikin aka tabbatar da shi.

Kungiyar ta yi nasarar daukar kofin Premier sau biyar da kuma na Zakarun Turai a 2008 bayan da iyalan Glazern su ka saye ta.

Karin bayani