Najeriya da Scotland sun yi 2-2

Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Najeriyar na kokarin zabar 'yan wasa 23 daga cikin 30 da za ta je gasar kofin duniya da su

Najeriya da Scotland sun tashi kunnen doki 2-2 a wasan sada zumunta da suka yi a filin wasan Fulham da ke London.

Dan wasan Scotland Charlie Mulgrew ne ya fara daga ragar Najeriya minti goma da fara wasa, kafin Uchebo ya rama a minti na 41.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 52 dan wasan Najeriyar Azubuike Egwuekwe ya ci kansu.

Ana dai dai da lokacin tashi ne a minti na 90 kuma sai Najeriyar ta rama kwallo ta biyu ta hannun Uche Nwofor.

Wasannin sada zumunta

Sauran wasannin da aka yi ranar Larabar nan, Amurka 2-0 Azerbaijan; Korea ta Kudu 0-1 Tunisia

Denmark 1-0 Sweden.

Wasannin da za a yi ranar Alhamis sun hada da Mexico da Israel; Kamaru da Paraguay; Saudi Arabia da Georgia.