Onazi ya tsallake rijiya da baya a Jos

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ogenyi Onazi a wasan Nigeria da kasar Mexico

Dan kwallon Nigeria, Ogenyi Onazi ya ce ya tsallake rijiya da baya, sakamakon bam din da ya hallaka mutane da dama a Jos na jihar Filaton Nigeria.

Bam din ya hallaka mutane kusan 118 a kusa da kasuwar Terminus.

Onazi mai shekaru 21 wanda haifaffen birnin Jos ne, ya bar kasuwar a ranar Talatar makon jiya kuma jim kadan sai bam din ya fashe.

Dan wasan mai taka leda a Lazio ya ce "Ina ganin cewar na yi matukar sa'a. Allah ne ya kare ni".

Onazi ya ce "Mun je kasuwar muyi siyayya kuma mintuna 15 da muka bar kasuwar sai muka ji kara mai karfi, sai mutane suka soma gudu".

A yanzu haka Onazi na London domin bugawa Super Eagles kwallon a wasan sada zumunci da Scotland.