Minista ya nemi a hana PSG shiga gasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ministan ya ce, '' babu wata maganar cin tara, kamata ya yi kawai a hana kungiyar shiga gasar Zakarun Turai''

Ministan nakasassu na Birtaniya Mike Penning ya nemi Uefa ta hana PSG shiga gasar Zakarun Turai idan an samu magoya bayanta da laifin cin zarafin magoya bayan Chelsea nakasassu.

Magoya bayan Chelsea nakasassu biyar da masu kula da su, sun ce an tofa musu yawu da jifansu da chingam da robobin ruwa a lokacin wasansu a Paris ranar biyu ga watan Afrilu.

Ministan ya ce, '' babu wata maganar cin tara, kamata ya yi kawai a hana kungiyar shiga gasar.''

Ya kara da cewa,'' ina ganin idan suna cikin gasar Zakarun Turai a shekara mai zuwa kamata ya yi a duba yuwuwar hanata.''

PSG za ta iya fuskantar hukuncin hana magoy bayanta shiga wani bangare na filin wasansu a lokacin wasa idan an laifin ya tabbata, a ranar 17 ga watan Yuli da ake tsammani Uefa za ta yanke hukunci.

Chelsea ta yi rashin nasara a karonsu na farko na wasan na dab da na kusa da karshe a Paris amma kuma ta yi nasara a karo na biyu har ta kai wasan kusa da karshe a gasar.