Tennis: An yi waje da Serena Williams

Serena Williams Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Serena 'yar Amurka mai shekaru 32 ta tafka kurakurai 29 a wasan

Mai rike da kofin gasar tennis ta Faransa Serena Williams, ta bi sahun 'yar uwarta Venus wajen ficewa daga gasar bayan da Garbine Muguruza ta Spain ta yi waje da ita a rana ta hudu da ci 6-2 6-2.

Daman yayar Serenan Venus Williams mai shekaru 33 ta sha kashi a hannun Anna Schmiedlova 'yar kasar Slovakia mai shekaru 19 da ci 2-6 6-3 da 6-4 a gasar ta Roland Garros.

Wannan dai shi ne karon farko da Serena ta kasa kaiwa mako na biyu na wata babbar gasa a matsayinta na ta daya a wasan tennis a duniya.

Yanzu dai za a hadu ne tsakanin Muguruza mai shekaru 20 da Schmiedlova a zagaye na uku maimakon Serenan da kanwarta.

Djokovic da Roger Federer

A bangaren maza kuwa Novak Djokovic da Roger Federer sun tsallake zuwa zagaye na uku na gasar ta Roland Garros da nasara a turmi uku kowanne.

Djokovic na daya a duniya ya dauki mintuna 90 ne kawai ya yi waje da Jeremy Chardy da ci 6-1 6-4 6-2.

A zagayen 'yan 16 da za a shiga Djokovic zai hadu da na 25 Marin Cilic dan Crotia wanda ya doke Tobias kamke na Jamus.

Shi kuwa Roger Federer zakaran gasar ta Faransa na 2009 ya doke Diego Sebastian Schwartzman ne da ci 6-3 6-4 6-4.

Roger dan Switzerland zai kara a zagaye na uku da na 31 a Rasha Dmitry Tursunov