Suarez ya ce zai iya wasa- Johnson

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Suarez ya kuma samu kyautukan zakaran kungiyar kwararrun 'yan wasa da ta marubuta wasanni na bana

Dan wasan Ingila Glen Johnson, ya ce takwaransa na Liverpool kuma dan Uraguay Louis Suarez, ya gaya masa cewa zai sami lafiyar da zai iya wasan kofin duniya da za a yi tsakanin kasashensu ranar 19 ga watan Yuni.

Suarez mai shekaru 27, wanda ake shakkun buga wasansa a rukuni na hudu wato Group D, saboda tiyatar da aka masa a gwiwa ranar Alhamis, ana sa ran warkewarsa bayan kwanaki 15 ko makonni hudu.

Johnson mai shekaru 27 ya ce "na yi magana da Suarez cikin wannan makon nan kuma ya ce baya ganin abin ya yi tsananin da ba zai iya gasar ba.''

Suarez ya fi kowa cin kwallaye a gasar premier da ta kare inda yake da kwallaye 31, duk da rashin buga wasanni biyar a farkon gasar saboda hukuncin dakatarwa.