UEFA na tuhumar Diego Simeone

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Diego Simeone ya kutsa cikin fili

Hukumar kwallon Turai UEFA na tuhumar kocin Atletico Madrid Diego Simeone da aikata laifi saboda kutsawa cikin fili a wasan karshe na gasar Zakarun Turai.

Simeone ya shiga cikin fili har sau biyu a wasan da kungiyarsa ta sha kashi a hannun Real Madrid da ci hudu da daya a Lisbon.

Daga bisani alkalin wasan Bjorn Kuipers ya kori Simeone daga cikin fili.

Haka kuma UEFA din na tuhumar Xabi Alonso na Real Madrid da laifin aikata ba dai-dai ba bayan kamalla wasan.

A ranar 17 ga watan Yuli, UEFA za ta saurari tuhumar aikata rashin da'a a kan Simeone da Alonso.