Van der Vaart ba zai je Brazil ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rafael van der Vaart tsohon dan kwallon Tottenham

Dan wasan tsakiya na kasar Netherland Rafael van der Vaart, ba zai buga gasar cin kofin duniya ba saboda raunin da ya samu a lokacin horo.

Dan wasan mai shekaru 31, wanda kuma ya ci kwallaye 109, shi ne mafi kwarewa daga cikin 'yan kwallo 30 na kungiyar da kocin kasar Louis van Gaals ya fitar don tinkarar gasar.

Van der Vaart, ya yi wasa a gasar cin kofin duniya a shekarar 2006 da 2010, amma ba ya cikin 'yan wasa 23 da za a tatantance a karshe da za a bayyana sunayensu a ranar Asabar.

Dutch dai tana cikin rukuni na biyu a gasar tare da kasar Spain da Chile da kuma Australia.

'Yan wasan da Holland ta gayyata:

Masu tsaron gida: Jasper Cillessen (Ajax), Tim Krul (Newcastle), Michel Vorm (Swansea), Jeroen Zoet (PSV Eindhoven).

'Yan baya: Daley Blind, Joel Veltman (both Ajax), Stefan de Vrij, Daryl Janmaat, Terence Kongolo, Bruno Martins Indi, Tonny Vilhena (all Feyenoord), Karim Rekik (PSV Eindhoven - on loan from Manchester City), Patrick van Aanholt (Vitesse Arnhem), Paul Verhaegh (FC Augsburg), Ron Vlaar (Aston Villa).

'Yan tsakiya: Jordy Clasie (Feyenoord), Jonathan de Guzman (Swansea), Nigel de Jong (AC Milan), Leroy Fer (Norwich), Arjen Robben (Bayern Munich), Wesley Sneijder (Galatasaray), Georginio Wijnaldum (PSV Eindhoven).

'Yan Gaba: Jean-Paul Boetius (Feyenoord), Memphis Depay (PSV Eindhoven), Klaas-Jan Huntelaar (Schalke 04), Dirk Kuyt (Fenerbahce), Jeremain Lens (Dynamo Kiev), Quincy Promes (Twente), Robin van Persie (Manchester United).