Za a bai wa 'yan Kamaru dala dubu 104

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption kyaftin din Kamaru, Samuel Eto'o

Hukumar kwallon Kamaru da gwamnatin kasar sun amince su bai wa 'yan kwallon kasar dala dubu 104 kowannensu, domin buga gasar cin kofin duniya.

Hakan kari ne daga abinda aka baiwa 'yan kwallon a lokacin gasar da aka buga a Afrika ta Kudu a shekara ta 2010.

An cimma yarjejeniya kan kudin da za a baiwa 'yan kwallon ne bayan wata doguwar tattaunawa kan batun.

Kocin Kamaru, Volker Finke ya ce babu ruwansa da batun kudin 'yan kwallon, hankalinsa na batun murza leda ne.

Finke ya ce "Ina son ina maida hankali a kan kwallo ne, batun kudi na tsakanin 'yan wasa da hukumominsu".