Poyet na nan daram a Sunderland

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Gus Poyet ya ce zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa

Kocin Sunderland Gus Poyet ya sabunta kwantaraginsa a kungiyar har zuwa shekarar 2016.

Poyet ya sanya kungiyar ta yi rawar gani a gasar Premier musamman daga karshe, inda suka yi nasara sau hudu a jere.

Haka kuma ya sanya kungiyar ta kai wasan karshe a gasar cin kofin League.

Poyet , mai shekaru 46, ya shaidawa shafin intanet na kungiyar cewa " a jima ana yi sai gaskiya. Wannan kwantaragi da na sabunta za ta ba ni damar kara kaimi, sannan kungiyar za ta samu alkibla''.

Karin bayani