Arsenal ta sake daukar Kofi

Image caption Kungiyar Arsenal ta mata ta yi kaka-gida a gasar kofin FA ba kamar ta maza ba wadda a bana ta dauka

Kungiyar Arsenal ta sake daukar kofin hukumar kwallon kafa ta Ingila FA na mata bayan ta buge Everton 2-0.

Matan na Arsenal sun dauki kofin ne a karo na biyu a jere wanda kuma ya kasance na 13 da suke dauka.

Arsenal din ta yi nasarar daukar kofin sau 12 a shiga gasar da ta yi sau 13 a baya.

Kelly Smith ce ta fara cin Everton a minti 15 da shiga fili, kafin Yukari Kinga ta kara ta biyu a dai-dai minti 60 na wasan.