Kofin Duniya : Qatar na tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Qatar za ta iya rasa damar karbar bakuncin gasar ta Kofin Duniya ta 2022

Mataimakin shugaban Fifa Jim Boyce ya ce zai ba da goyon baya a sake kuri'ar zaben kasar da za ta karbi bakuncin gasar Kofin Duniya ta 2022 idan an samu Qatar da laifin ba da cin hanci.

Jaridar Sunday Times ta yi zargin cewa wasu jami'an Fifa sun karbi cin hanci na fam miliyan uku domin goyon bayan Qatar.

Tuni babban mai bincike na Fifa Micheal Garcia ya shiga gudanar da bincike kan zargin.

Amma kwamitin nema wa Qatar damar karbar bakuncin gasar ya musanta zargin.

Jaridar ta ce ta samu takardu na sirri da ke nuna cewa tsohon jami'in Fifa kuma tsohon shugaban hukumar kwallon Asia, Mohammed bin Hammam ya bai wa jami'an Fifa kudade domin goyon bayan Qatar.