Tennis: Nadal zai kara da Ferrer

Hakkin mallakar hoto x
Image caption Shi kuwa David Ferrer ya lallasa Kevin Anderson da ci 6-3 6-3 6-7 6-1

Rafeal Nadal ya ci gaba da kokarin daukar kofi na biyar a jere na gasar Faransa inda ya kai wasan dab da na kusa da karshe.

Dan wasan na daya a duniya ya kai wannan matakin ne bayan da ya yi galaba a kan Dusan Lajovic da ci 6-1 6-2 6-1.

Nadal mai shekaru 27 ya yi waje da Lajovic dan Serbia cikin minti 93 kawai.

A wasan dab da na kusa da karshen da za a yi ranar Laraba, za a maimaita wasan karshe na bara inda Nadal zai hadu da David Ferrer wanda ya yi waje da Kevin Anderson.